A shekarar da ta gabata, yara dubu 13,600 da ba sa tare da iyayensu ne suka nemi mafaka a kasashen Tarayyar Turai.
Dangane da bayanan Ofishin Hukumar Kididdiga ta Turai (Eurostat), kashi 10 cikin 100 na yaran kanana ne da basa tare da iyayensu daga cikin ‘yan kasa da shekaru 18 da suka nemi mafaka a kasashen Turai.
Daga cikin wadannan masu neman mafakan, kaso 88 daga darinsu maza ne, kaso 67 cikin 100 an bayar da rahoton cewa suna tsakanin shekaru 16 zuwa 17, kaso 22 'yan tsakanin shekaru 14 zuwa 15 ne, haka kuma kaso 11 cikin dari 'yan kasa da shekaru 14 ne.
Kashi biyu bisa ukun yaran da ba sa tare da kowa sun tafi kasashen Turai daga Afghanistan, Syria da Pakistan.
Kasashen da waɗannan yara suka fi nema mafaka sune Girka da Jamus. Kashi 20 cikin 100 na kananan yara wadanda ba sa tare da kowa sun nemi mafaka a Girka, kashi 16 a Jamus, kashi 10 a Austria da 9 a Belgium.
Adadin yaran da ke neman mafaka a kasashen Turai ba tare da wani mai kula dasu ba yana raguwa tun daga shekarar 2015. Wannan adadin, wanda yakai dubu 92 a shekarar 2015, ya ragu zuwa dubu 14 da 100 a shekarar 2019.