Yara a Holland za su iya amfani da Euthanasia "kashe kai"

Yara a Holland za su iya amfani da Euthanasia "kashe kai"

A Netherlands gwamnati ta amince da shirin ba da izinin Euthanasia wato “kashe kai” ga yara daga shekara 1 zuwa 12 masu cutar ajali.

Dangane da rahoton BBC, Ministan Lafiya na Holland, Hugo de Jonge a cikin wasikar da ya aike wa Majalisa ya bayyana cewar shirin da gwamnati ta amince da shi zai hana wasu yara shan wahala "azaba da ba za a iya jurewa ba". 

De Jonge ya bayyana cewar binciken da masana suka gudanar ya nuna cewa ana bukatar irin wannan ka’idar game da Euthanasia, kuma ba za a sauya dokokin yanzu ba kuma za a kare likitoci daga gurfanar a gaban shari’a idan sun amince da Euthanasia a yaran wannan shekarun.

Ministan Kiwon Lafiya na Holland ya kuma bayyana cewar ana tunanin yara 5 zuwa 10 daga ’yan shekaru 1 zuwa 12 za su amfana daga Euthanasia a kowace shekara.

A Netherlands, doka ta yarda da Euthanasia ga yara sama da shekaru 12 da jarirai 'yan ƙasa da shekara 1, tare da yardar mara lafiyan da danginsa da yardar aƙalla likitoci 2.

Wannan shirin ya haifar da cece-kuce na tsawon watanni tsakanin gwamnatin hadaka ta jam’iyyu 4 da ke mulki. Jam’iyyar Kristoci masu ra’ayin rikau sun yi matukar adawa da shirin. 


News Source:   ()