Watan Yuli da ya gabata, ya kasance wata na biyu mafi zafi a tarihin Turai kuma na uku mafi zafi a duk duniya.
Watan Yuli mafi zafi a Turai na karshe ya kasance a cikin shekarar 2010. A cewar masana kimiyya na Turai, an yi rikodin Yuli na biyu mafi zafi a nahiyar a wannan shekarar.
Dangane da Hukumar Canjin Yanayi ta Tarayyar Turai, Copernicus, bayan shekarun 2019 da 2016, Yulin shekarar 2021 ya kasance Yuli na uku mafi zafi a duniya.
An samu iska mai zafi da ya mamaye Turai a watan da ya gabata daga Baltic zuwa gabashin Bahar Rum.
Sakamakon hakan, an samu matsakaicin gobarar daji 200 a mako guda da suka barke a Faransa da Spaniya.
Wasu sassan Amurka kuma sun fada cikin bala'in fari da ya kafa tarihi.
Masana kimiyyar Copernicus sun bayyana cewa matsanancin yanayin zafi ya mamaye wasu yankuna na Arewacin Amurka kuma yanayin bushewan daji ya ƙarfafa yaduwar gobarar daji.