'Yan tawayen Syria sun ƙaddamar da munanan hare-hare kan dakarun gwamnati

'Yan tawayen Syria sun ƙaddamar da munanan hare-hare kan dakarun gwamnati

Karon farko kenan da ‘yan tawayen suka samu damar tun bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki a shekarar 2020.

Kungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Syrian Observatory mai hedikwata a Birtaniya, da ke sa ido kan yaƙin ƙasar ta Syria ta ce ya zuwa wannan Alhamis mayaƙa da kuma dakaru daga ɓangarorin biyu, fiye da 130 aka kashe yayin gumurzun da rahotanni ke cewa har yanzu bai lafa ba.

Masu sa idon sun ce ‘yan tawayen na Syria sun haɗa gwiwa ne da mayaka masu iƙirarin jihadi na ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham, wajen ƙaddamar da hare-haren bazatar kan sojojin gwamnati jiya Laraba a lardin Aleppo dake arewacin ƙasar.

Wasu majiyoyi daga cikin Syrian sun ce ya zuwa lokacin wannan rahoton mayaƙan ƙungiyar Hayat Tahrir 65 aka kashe, 18 daga ɓangaren ‘yan tawaye, yayin da sojojin gwamnati suka rasa dakaru 49.

Ƙungiyar Hayat Tahrir dake da alaƙ da Al-Qa’eda na iko da akasarin yankin arewa maso yammacin Idlib, babban birnin lardin na Aleppo, gami da wasu ƙarin yankuna a lardunan Hama da Latakia.

A watan Maris na 2020, Rasha da Turkiya suka jagoranci ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen Syria a Aleppo, lamarin da ya sassauta yaƙin basasar da ya laƙume rayukan mutane fiye da dubu 500 a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)