Lardin Balochistan mai arzikin ma'adinai mai iyaka da Iran da Afganistan, ya kasance yankin da 'yan kabilar Baloch 'yan aware suka yi tawaye tsawon shekaru goma.
Akalla sojoji 18 da maharan dauke da makamai 24 ne suka mutu a wasu al’amura biyu masu alaka da su a kudu maso yammacin Pakistan, kamar yadda jami’ai da kafafen yada labaran kasar suka bayyana, yayin da rikicin addini, kabilanci da kuma na ‘yan aware ke kara ta’azzara a yankin.
Rundunar sojin Pakistan a ranar Asabar din da ta gabata ta ce mayakan sun yi yunkurin kafa shingayen kan hanya a cikin dare a lardin Balochistan mai fama da rikici, a yayin wasu da dama daga cikin su suka mutu a yayin da aka far musu.
Wani jami'in 'yan sanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wata mota dauke da jami’an tsaron sa kai na Frontier Corps marasa makami a kusa da garin Mangochar ta fuskanci luguden wuta daga mahara 70 zuwa 80 da suka tare hanya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI