'Yan tawaye na ci gaba da kwace ikon garuruwa a kasar Syria

'Yan tawaye na ci gaba da kwace ikon garuruwa a kasar Syria

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyoyi masu alaka da kasar Iran, wandanda ke marawa gwamnati baya tun a shekarar 2015, suka karkata akala kan yakin da ke faruwa a Lebanon da Gaza.

Rahotanni sun ce, hare-haren sama sun tilasatawa mazauna kauyuka da dama nemanrwa kansu mafaka

Da dama daga cikin masu dauke da makaman ma, bayanai sun ce suna dab da shiga birnin Aleppo, abin da ya kai musayar wuta tsakaninsu da dakaarun gwamnati

Karon farko Kenan da masu adawa da gwamnati suka kaiwa birnin hari tun shekarar 2016, wato lokacin da dakarun gwamnatin Syria da ke samun goyon bayan kasashen Rasha da Iran suka fatattake su daga gabashin birnin

Rundunar sojin Syria ta fitar da wata sanarwar cewa, dakarunta na artabu da masu tayar da kayar baya a wajen birnin Aleppo da kuma Idlib, inda suka lalata makamai tare da kakkabo jiragen marasa matuka.

Hizbullah, wadda ke samun goyon bayan Iran wadda kuma ke mara baya ga gwamnatin Syria, ta shiga fagen daga da dakarun Isra’ila tun a watan Satumba, abin da ake ganin ya bawa masu dauke da makaman tunkarar gwamnati.

A ranar Laraba aka sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin dakarun Hizbullah da na Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)