'Yan takarar shugabancin Amurka na tafiya kunnen doki a kuri'un da aka kaɗa zuwa yanzu

'Yan takarar shugabancin Amurka na tafiya kunnen doki a kuri'un da aka kaɗa zuwa yanzu

Zaɓen na bana ana ganin yana cikin masu matukar tarihi da kuma rikitarwa, ganin yadda ƴan takarar ke tafiya kusan kunnen doki a zaɓen jin ra’ayoyin jama’a da aka kaɗa.

Ƙididdiga na nuna cewa kowanne ɗan takara tsakanin Donald Trump na Republican da kuma Kamala Harris ta Democrats na da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen ganin yadda ake ci gaba da gwabzawa.

Tuni dai aka kaɗa kuri’u sama da miliyan 82, yayinda aka fi mayar da hankali kan jihohi 7 da ke da matuƙar tasirin da zasu iya sauya alƙaluman zaɓen.

Jihohin dai sun haɗar da Arizona, Georgia, Michigan, Nevada, North Carolina, Pennsylvania, da Wisconsin, kuma ana ganin cewa duk ɗan takarar da ya sami nasara a waɗannan jihohi, tabbas zai yi wahala ya kasa lashe zaɓen.

Ana ganin shiga zaɓe tsakanin Trump farar fata da ke da akidar kin jinin baki da kuma Kamala Haris bakar fata kuma mace na kara zafafa zaben, wanda ya nuna karara cewa zabe ne tsakanin bakar fata da kuma farar fata, da zai baiwa Kamala damar kafa tarihi.

A nasa ɓangare kuma Trump na yunkurin kafa tarihin zama shugaba na farko a Amurka da yayi shugabanci sau biyu a mabanbantan lokuta .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)