An sanar da cewa ‘yan ta’addan PKK a arewacin Siriya wato YPG sun hallaka farar hula biyu sakamakon tashin bam din da suka haka a yankin.
An tabbatar da cewa bam din ya tashi ne a wani gida dake wani kauye tsakanin inda Dakarun Siriya na NSA suke da kungiyar ta’addar YPG a gundumar Tal Abyad.
Kamar yadda al’umman yankin suka sanar mutanen biyu burbudin kasa ta taushesu wadanada suka yi yunkurin kubutar dasu kuma an kai musu hari da gurnati.