A watan da ya gabata ne Kungiyar dalibai da wasu kungiyoyin kare hakokin ma’aikata a kasar suka shirya zanga-zangar nuna adawa da kason aikin ma'aikata wanda ya rikide zuwa kisa bayan wani farmakin da 'yan sanda suka kai, inda aka kashe mutane 206 a cikin kwanaki na tashin hankali kamar yadda alkaluman 'yan sanda da na asibiti na AFP suka nuna.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Bangladesh AP - Rajib DharMataimakin kwamishina Junaed Alam Sarkar ya tabbatar da sallamar wadanan dalibai da ake tsare da su ga iyalansu. A ranar Juma’ar da ta gabata ne jami’an tsaro na farin kaya suka kama Nahid Islam Shugaban dalibai da wasu mutane biyu a wani asibiti da ke Dhaka babban birnin kasar, inda aka kama su,aka kuma isa da su wani wuri da ba a sani ba. Mahaifinsa Badrul Islam ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa Nahid ya koma gida ne da yammacin yau Alhamis.
Yan Sanda na tarwatsa masu zanga-zanga a Bangladesh REUTERS - Mohammad Ponir HossainAn kuma tsare wasu mutane uku inda gwamnati ta ce a lokacin an tsare su ne domin kare lafiyarsu. Ministan shari'a Anisul Huq ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa a yau Alhamis cewa dukkaninsu shida sun ba da kansu don kasancewa a hannun 'yan sanda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI