'Yan sanda sun ce da safe "tawagar bincike ta musamman" da suka hada da hukumar 'yan sanda ta kasa, hukumar 'yan sanda ta Seoul da kuma sashin tsaro na majalisar dokokin kasar ba su sami damar shiga babban ginin ba saboda hana shiga da jami'an tsaron fadar shugaban kasa suka yi," in ji daya daga cikin jami’an.
Daga Fadar shugaban kasa ba a kai ga samun karin haske danagane da wannan yukunri ba, Yoon Suk Yeol ya ba wa kasar mamaki ta hanyar kafa dokar soji ba zato ba tsammani a daren ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamba, kafin a tilasta masa soke ta bayan sa'o'i shida bayan matsin lamba daga majalisar dokoki da kuma jama’a da suka fito.
Shugaban kasar da kyar ya tsallake rijiya da baya ga kudirin korar da majalisar dokokin kasar ta gabatar, wanda jam’iyyarsa ta ceto.
A ranar Laraba da ta gabata hukumomin kasar suka bayar da rahoton cewa, tsohon ministan tsaro a ofishin a lokacin da aka kafa dokar ta-baci, Kim Yong-hyun, ya yi yunkurin kashe kansa a gidan yari, mintuna kadan kafin a kama shi a hukumance ta hanyar bayar da sammaci a kansa.
An zarge shi da taka muhimmiyar rawa a lokacin tawaye da kuma aikata "cin zarafi don kawo cikas ga gudanar da 'yancin", ya riga ya kasance a tsare tun ranar Lahadi amma ya zama dole don tsawaita shi.
Ma’aikatar shari’a da wani jami’in gidan yari sun ce yana nan lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI