Yakin Gaza: Wasu ranakun da ba za a mance da su ba

Yakin Gaza: Wasu ranakun da ba za a mance da su ba

Albarkacin cika shekara guda na barkewar wannan tashin hankali, za muyi dubi kan wasu daga cikin ranakun da ba za a mance da su ba a wannan yaki na yankin Gabas ta Tsakiya.

7 ga Oktoban 2023

Da misalin ƙarfe 6 da rabi ne dai mayaƙan Hamas suka kai munanan hare-hare cikin Isra’ila, wanda yayi sanadiyar mutuwar Yahudawa dubu 1 da 189 da yin garkuwa da wasu 251, lamarin da ya sanya Faraministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bayyana cewar ƙasar ta tsunduma cikin yaƙi.

Daya daga cikin waɗanda harin Hamas ya rutsa da su a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba 2023. Daya daga cikin waɗanda harin Hamas ya rutsa da su a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba 2023. AP - Tsafrir Abayov

8 ga Oktoban 2023

A ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2023, Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya a yankin Gaza, bayan da ta hada dakaru kusan dubu ɗari 3.

9 ga Oktoban 2023

Kwana ɗaya da ƙaddamar da hare-haren, a ranar 9 ga watan Oktoban shekarar 2023, Isra’ila ta kammala mamaye yankin Gaza da ke da yawan Falasdinawa miliyan biyu.

13 ga Oktoban 2023

A ranar 13 ga watan Oktoban ne kuma Isra’ila ta bai wa mazauna yankin zirin Gaza wa’adin sa’oi 24 da su fice daga gidajensu, abinda ya sa wasu suka yi biyayya domin tsira da rayukansu wajen komawa Kudancin yankin, amma wasu kuma suka ƙi ficewa daga gidajen su.

17 ga Oktoban 2023

Ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2023, rana ce da baza a mance da ita a wannan rikici ba, domin a ranar  ce aka samu wata fashewa a asibitin Al-Ahli da ke birnin Gaza inda ma’aikatar kula da lafiyar yankin ta ce mutane 471 ne suka mutu, yayin da majiyoyin leken asirin Amurka ke cewa adadin bai kai haka ba.

Harabar asibitin Al-Ahli da Isra'ila ta kai a ranar 17 ga watan Oktoban 2023. Harabar asibitin Al-Ahli da Isra'ila ta kai a ranar 17 ga watan Oktoban 2023. © AP / Abed Khaled

Hamas da kawayenta sun zargi Isra’ila da kai wannan hari wanda tuni ta musanta, yayin da wasu kafafen yada labarai ke ganin cewa an samu kuskure ne wajen harba makamin roka a Gaza wanda ya haifar da fashewar. Cikin masu cewa makamin Hamas ne ya yi kuskuren afkawa asibitin harda shugaban Amurka Joe Biden, bayan duniya ta kadu da kuma Allah wadai da harin.

27 ga Oktoban 2023

A wannan ranar ce Isra’ila ta ƙaddamar da kai hare-hare ta ƙasa a yankin Gaza, wadda ta ke ganin ta hakan ne za ta lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da mayaƙan Hamas ke amfani da su wajen yin zirga-zirga da kuma samun mafaka.

15 ga Nuwamba 2023

15 ga watan Nuwambar shekarar 2023, rana ce da ba za a mance da ita a wannan yaki ba, domin a wannan ranar ce Isra’ila ta mamaye asibitin Al-Shifa, wanda shine mafi girma a yankin Gaza, bayan da ta yi zargin cewa mayaƙan Hamas na amfani da ginin asibitin a matsayin cibiyar ta. Kwanaki uku sojojin Isra’ila suka kwashe a wannan waje ana dauki ba dadi, daga nan kuma suka hari wasu asibitocin dake yankin.

24 ga Nuwamba zuwa 1 ga Disamba 2023

A wannan tsakani ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, a ƙarkashin wannan yarjejeniyar ce kuma aka samu nasarar yin musayar fursunonin yaki, inda Hamas ta saki mutane dari da 5 da ke da shedar zama ƴan ƙasashe biyu, ita kuma Isra’ila ta saki Falasdinawa 240 da ta ke tsare da su a gidan yari. Haka kuma anyi amfani da damar wajen shigar da kayan agaji yankin Gaza domin tallafawa Falasdinawan da suka tagayyara.

5 ga Disamba 2023

A wannan rana ce Isra’ila ta ƙaddamar da gagarumin hari ta ƙasa a yankin  da ke kudancin Gaza, wajen da daruruwan Falasdinawa ke samun mafaka, inda ta buƙace su da su ƙara matsawa can kusa da iyaƙar Rafah.

Yadda yankin Khan Younis, ya koma bayan hare-haren Isra'ila. Yadda yankin Khan Younis, ya koma bayan hare-haren Isra'ila. AP - Abdel Kareem Hana

 

15 ga Disamba 2023

Sojojin Isra’ila suka harbe uku daga cikin mutanen da Hamas ta kama waɗanda suka tsere daga wajen da ake tsare da su, wannan lamari dai ya fusata ‘ƴan uwan waɗanda ke hannun mayaƙan Hamas, inda suka buƙaci gwamnatin Isra’ila ta sake ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

2 ga watan Janairu 2024

A ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2024, Isra’ila ta kashe Saleh al-Arouri, mataimakin shugaban ƙungiyar Hamas mai kula da harkokin siyasa a wani hari da ta kai kudancin birnin Beirut na Lebanon.

23 ga watan Janairu 2024

A karon farko Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da barazanar ɓarkewar yunwa a yankin Gaza.

29 ga Fabarairu 2024

Aƙalla mutane 118 suka rasa ransu wasu 760 suka samu raunuka, a wani hari da Hamas ta zargi Isra’ila da kaiwa wajen da ake rabon kayan abinci a Gaza, sai dai Isra’ila ta ce tayi harbi ne kan mutanen da ke sace kayayyaki.

12 ga Maris 2024

A wannan ranar ce Isra’ila ta hana wani jirgin ruwa da ke ɗauke da kayan abinci tan dari 2 da ya taso daga Cyprus wucewa, kwana biyu da fara Azumin watan Ramadan, matakin da ya gamu da suka daga wasu kasashe.

1 ga Afrilu 2024

Sojojin Isra’ila sun kai hari kan tawagar ƙungiyar ‘World Central Kitchen’ ta ƙasar Amurka, wacce ke aikin raba kayan abinci ga mabukata a yankin Gaza, sai dai daga bisani Isra’ila ta amsa laifinta inda ta ce bisa kuskure ne ta kai harin.

 

A view of a vehicle where employees from the World Central Kitchen (WCK), including foreigners, were killed in an Israeli airstrike, according to the NGO as the Israeli military said it was conducting Motar agajin da Isra'ila ta kaddamar wa hari a Gaza. REUTERS - Ahmed Zakot

 

A wannan rana ce kuma Isra’ila ta kai hari ofishin jakancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Syria, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar dakarun juyin juya hali 7 cikin su har da Janar Reza Zahedi.

13 ga Afrilu 2024

A wannan rana ce Iran ta maida martani ta hanyar harba kuramen jirage masu sarrafa kan su sama da dari 3 kan Isra’ila, wanda shi ne karo na farko da ƙasar ta kai hari cikin Isra’ila tun bayan barkewar wannan yaki.

7 ga Mayu 2024

Sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a yankin Rafah da ake amfani da shi wajen ƙetarawa zuwa cikin Masar, bayan da ta nemi Falasdinawa su koma can domin kaucewa hare haren da take kai wa da sunan neman mayakan Hamas.

22 ga Mayun 2024

22 ga watan Mayu, rana ce da aka kafa sabon tarihi ganin yadda ƙasashen Ireland da Norway da kuma Spain suka amince da samar da ƙasar Falasdinu, tare da zargin Isra’ila da daukar duk wasu matakai na kin amincewa da yarjejeniyar Oslo ta shekarar 1993.

6 ga Yunin 2024

Sojojin Isra’ila sun kai hari makarantar UNRWA da aka maida shi sansanin ƴan gudun hijira a Nuseirat, bayan da suka yi iƙirarin cewa akwai kwamandojin mayakan Hamas da aka ɓoye a wajen. A wannan hari an kashe mutane 37 kuma an kuɓutar da mutune 4 daga cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su.

 

Makarantar UNRWA da ke Nuseirat a yankin Gaza, ranar 7 ga watan Yulin 2024. Makarantar UNRWA da ke Nuseirat a yankin Gaza, ranar 7 ga watan Yulin 2024. AFP - EYAD BABA

 

13 ga Yulin 2024

Wani harin jiragen sama da Isra’ila ta kai Khan Younis, yayi sanadiyar mutuwar Mohammed Deif shugaban ɓangaren mayaƙan Hamas na birget din Ezzedine da al-Qassam, wanda Isra’ila ke kallon shi a matsayin wanda ya kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba, bayan da ta shafe shekaru sama da 30 tana neman sa ruwa a jallo.

27 ga Yulin 2024

An harbo wasu makaman rokoki daga Lebanon zuwa cikin Isra’ila da yayi sanadiyar mutuwar Yahudawa 12. Wannan harin dai ana kallonsa a matsayin mafi muni da Isra’ila ta rasa fararen hula tun bayan na 7 ga watan Oktoba. Isra’ila ta zargi Hezbollah da kai harin, zargin da tuni ta ƙaryata.

31 ga Yulin 2024

A wannan rana ce aka kashe Ismail Haniyeh, wanda ke jagorantar ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas ta Falasdinawa, bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran Masoud Pezeshkian. An dai zargi Isra’ila da kai wannan hari, sai dai bata ce komai dangane da zargin.

 

Yadda aka gudanar da jana'izar Ismail Haniyeh. Yadda aka gudanar da jana'izar Ismail Haniyeh. © Vahid Salemi / AP

 

10 ga Agusta 2024

Isra’ila ta kai hari ta sama kan makarantar Al-Tabi’ee, inda Falasdinawan da aka raba da gidajensu ke samun mafaka. Mutane 93 ne suka mutu a wannan hari, kuma wasu da dama suka samu raunuka, amma Isra’ila ta ce ta kai harin ne bayan da ta gano mayaƙan Hamas na amfani da wajen a matsayin cibiya.

25 ga Agustan 2024

Mayaƙan Hezbollah suka harba makaman roka da kuramen jirage cikin Isra’ila. ƙungiyar ta ce ta kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya kan kisan Fuad Shukr da aka yi a Beirut a ranar 30 ga Yuli.

17 zuwa 18 ga Satumban 2024

A tsakanin waɗannan ranaku ne daruruwan na’urorin sadarwa Pages suka fashe a Lebanon da kuma Syria, inda akalla mutane 37, mafi yawancin kananan yara ne suka mutu, sannan wasu da dama suka samu raunuka daban daban.

 

Yadda motocin ɗaukar marasa lafiya suke kai wadanda suka raunuka asibitin koyarwa na Beirut bayan fashe-fashen na'urorin sadarwar da aka samu a Lebanon a ranar 17 ga watan Satumba 2024. Yadda motocin ɗaukar marasa lafiya suke kai wadanda suka raunuka asibitin koyarwa na Beirut bayan fashe-fashen na'urorin sadarwar da aka samu a Lebanon a ranar 17 ga watan Satumba 2024. REUTERS - Mohamed Azakir

 

22 ga Satumban 2024

Isra’ila da Hezbollah suka fara musayar wuta a tsakanin su, ya yin da bayan kwana ɗaya kuma Isra’ilar ta buƙaci mutanen da ke zaune a kudancin Lebanon su fice daga cikin gidajen su.

28 ga Satumban 2024

A wannan rana ce Isra’ila ta kai hari Beirut, inda ta lalata akalla gidaje 6, kuma a wannan hari ne aka kashe jagoran ƙungiyar Hezbollah Sheikh Hassan Nasrallah da ya jagorancin kungiyar na sama da shekaru 30.

1 ga watan Oktobar 2024

A wannan ranar ce yakin Isra’ila da Hamas ya sake daukar sabon salo, sakamakon yadda kasar Iran ta harbawa Isra’ila makamai masu linzami sama da 200. Wannan mataki ya haifar da wani sabon tashin hankali sakamakon fadadar yakin da kuma fargabar cewar yana iya karade daukacin Gabas ta Tsakiya.

 

Hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kaiwa Isra'ila a ranar 1 ga watan Oktoba 2024. Hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kaiwa Isra'ila a ranar 1 ga watan Oktoba 2024. REUTERS - Amir Cohen

 

2 ga watan Oktobar 2024

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce suna nazari dangane da matakin da za su dauka na mayar da martani a kan kasar Iran. Netanyahu ya zargi Iran da zama dandalin ayyukan ta’addanci, tare da bayyana cewar kawar da shugabannin ta ne kawai zai tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

4 ga watan Oktoba 2024

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce suna tattauna wa da Firaministan Israila dangane da martanin da za ta mayar wa Iran, amma ya ce idan hurumin a hannunsa ya ke ba zai kai hari cibiyoyin da ake zargin Iran na gina makamin nukiliya ko kuma rijiyoyin hakar man ta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)