A yayinda Turkiyya ke cigaba da yaki da ta'addanci, rundunar sojin kasar da hadin kan jami'an leken asirin kasar na cigaba da daukar matakan kauda kungiyoyin ta'addanci da dama. A 'yan kwanakin nan ma an magance da yawan mambobin kungiyar ta'addar PYD/YPG a Siriya. A yayinda da kungiyar PYD/YPG ke samun goyon bayan Amurka a Siriya, Turkiyya na kara daukar matakan maganceta.
Akan wannan maudu'in mun sake kasancewa tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA…
Kungiyar ta'addar PKK wacce bayan Abdullah Ocalan ya kafata a tsakiyar shekarun 1970 ne ta fara alaka da wasu kungiyoyi a Siriya. Ta kara yawanta ta hanyar kafa kungiyoyi a Siriya. A lokacin gwamnatin Baban Bashar Asad ya horas da mambobin kungiyar a sansanin Beka dake Lebanon da zummar su kalubalanci Turkiyya, amma ganin irin yadda dakarun Turkiyya suka kalubalanci lamarin ya sanya shi ja da baya har ma da korar Ocalan da sauran mambobin kungiyar daga kasarsa. Sai dai a lokacin da aka fara yunkurin juyin juya hali a Siriya gwamnatin Asad ta sake kara amfani da kungiyar PKK domin kalubalantar Turkiyya da dakarun juya halin kasar ta hanyar yin hadaka da reshenta dake Siriya wato PYD/YPG, ya janye daga yankuna da dama tare da barinsu a hannun kungiyar ta'addar.
Yayin da kungiyar ta'addar ke haɓaka haɗin gwiwa tare da gwamnatin kasar, ta mallake ikon yankuna da dama a Arewacin Siriya, daga bisani kuma da sunan yaki da DEASH ta yi hadaka da Amurka lamarin da ya kara mata karfin gwiwa. Musanman a tsakiyar shekarar 2014 tallafi da gudunmowa da kungiyar PYD/YPG ta samu daga Amurka ya bata damar fadada ikonta a arewacin Siriya da kuma mallake da kuma kula da yankuna masu albarkatu da suka hada da Rakka da Deyr ez Zor tsakaninta da sojojin Amurka.
Babban muradinsu shi ne kame yankin Afrin da yankunan gabashin Siriya ta yadda zasu iya fadadawa zuwa gabashin Bahar Rum domin kafa wata karamar kasa mai iko. Sai dai farmakai da Turkiyya ta kaddamar bayan yunkurin juyin mulkin 15 ga watan Yuli da suka hada da Farmakin Garkuwar Firat da na Reshen Zaitun sun dakile wadancan manufofi. Haka kuma farmakin Tafkin zaman lafiya da ya biyu daga bisani ya sanya tsabtace Tel Abyad da Resulayn daga mambobin kungiyar ta'adda da kuma wargaza shirin PKK na kafa gwamnati. A wannan lokacin Turkiyya ta yi nasarar sanya sojojin Amurka janyewa daga yankin da kuma sanya wasu dakarun Rasha yada zango a wasu yankunan gabashin Firat.
Duk da irin wadannan matakan kungiyar ta'addar PYD/YPG na cigaba da kasancewa tun daga Tel Rifat a yammacin Rifat zuwa gabashin Firat da kuma Ayn al Arab a gabashin Firat zuwa Malikiye. Haka kuma ma a kudu masu gabashin kasar a yankin Rakka da Deyr ez zor. Turkiyya dai ta kasance wacce ke matsin lamba ga Amurka da Rasha domin magance ta'addanci a gefe guda kuma tana daukar kwararan matakan kauda yan ta'adda. Ta yi nasarar magance shugabanin kungiyoyin ta'addanci ta amfani da bayanan jami'an leken asirin kasar da kuma jiragenta marasa matuka. Turkiyya ta kuma kasance wacce ke hadaka da Larabawa da Kurdawan da suka kasance tsakiyar yan ta'adda domin magance ta'addanci.
Yayin da aka rage kungiyar 'yan ta'adda a Turkiyya, an takurawa kungiyoyin tare da ayyukan soji masu inganci a Iraki, kungiyar ta'addar na kokarin ci gaba da wanzuwa a karkashin kariyar Amurka a Siriya. Duk da haka, tare da fahimtar haka, Turkiyya na ci gaba da kai hare -hare masu gwabi dake nuna cewa Siriya ba ta kasance kasar da yan ta'adda zasu samu damar yin kaka gida ba.
Wannan sharhin Mal can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin siyasa, Tattalin arziki da Hallayar dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya. Ku huta lafiya...