Yaƙin Rasha da Ukraine ya sauya salo duk da fatan kawo ƙarshensa a mulkin Trump

Yaƙin Rasha da Ukraine ya sauya salo duk da fatan kawo ƙarshensa a mulkin Trump

A wani yanayi da duniya ke fatan kawo ƙarshen yaƙin na Rasha da Ukraine, ɓangarorin biyu sun ci gaba da kaiwa juna zafafan farmaki ko da ya ke harin na Ukraine a birnin Kazan cikin ƙarshen makon da ya gabata bai raunata kowa ba face lalata gine-gine, amma Vladimir Putin ya sha alwashin sake ragargazar Ukraine yana mai cewa ya zama masa wajibi rugurguza ƙasar fiye da yunƙurinta na ganin ta rusa Moscow.

Wani abu da ba a saba ganin faruwarsa a Turai ba wato harin ƙunar baƙin wake, da shi ne Ukraine ke amfani a baya-bayan nan don ganin ta rusa Rashar, a wani yanayi da ƙungiyar tsaro ta NATO ta karɓe ragamar bayar da makamai ga ƙasar daga Amurkawa don kaucewa barazanar da sabon shugaba Donald Trump ka iya zuwa da ita.

Dukkanin ɓangarorin biyu na ci gaba da amfani da ko dai Sojin haya ko kuma Sojin ƙasashe ƴan sakai da ke taimaka musu a yaƙin, sai dai wani batu da Moscow ke ci gaba da bayyanawa a matsayin farfaganda shi ne yadda dakarun na Putin ke ganin mummnar koma baya a fagen daga.

Ko a baya-bayan nan Korea ta kudu ta bayyana cewa akwai dakarun maƙwabciyarta Korea ta Arewa aƙalla dubu 1 da 100 da suka mutu a fagen daga yayin taimakawa Rashan a yaƙinta da Ukraine batun da ke jaddada kalaman Volodymyr Zelensky wanda ke cewa Pyongyang na ganin asarar dakaru a Kiev.

Bugu da ƙari wani batu da ke hadddasawa Rasha koma baya a wannan yaƙi na kusan shekaru shi ne yadda ta ke ganin masu cinna wuta da gangan ciki har da wasu 20 a baya-bayan nan, zagon ƙasar da kai tsaye Putin ya ɗora alhakinsa kan Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)