Wasu Yahudawa sun yi rubutun batanci ga Annabin Islama, Muhammadu (SAW), a wani bango dake yammacin Zirrin Gaza da Isra'ila ke mamaya.
A cewar kamfanin dillacin labarai na Falasdinu WAFA, Yahudawa farar hula masu mamaya sun ci mutuncin annabi Muhammadu (SAW) da taken Ibrananci inda suka yi rubutun cin mutuncin a bangon dake kusa da hanyar zuwa Bahar Mayit.
A cikin hotunan da suka bayyana a shafukan sada zumunta, an yada labaran cin mutuncin.
Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun rubuta taken yin batanci ga Annabi Muhammadu (SAW) yayin zanga-zangar "Tattaken Tuta" a ranar 15 ga watan Yuni mai tayar da hankali da aka gudanar a kofar Dimashka ta gabashin Urushalima da aka mamaye.
A gefe guda kuma, Magajin Garin Tuwana na garin Al-Halil, Muhammed Rib, ya sanar da cewa, Yahudawan fararen hula 'yan mamaya sun jejjefi wasu gidaje a garin lamarin da ya sanya mata biyu suka raunana.
Rib ya kuma bayyana cewa, wata kungiyar Yahudawa 'yan share wuri zauna sun yi wa wani Bafalasdine makiyayi duka a kusa da garin kuma ya kara da cewa sojojin Israila na yankin a lokacin da abubuwan suka faru, amma ba su hana Yahudawan aikata aika-aikan ba.