An sanar da cewa wasu gungun Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun kai farmaki a Masjidul Aksa a yayinda aka bude shi domin gudanar da ibada bayan ya kasance watanni biyu a rufe sanadiyar kwayar cutar Corona.
Dangane ga labaran da kafafen yada labaran cikin gidan kasar suka yada Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da suka sami rakiyar 'yan sandan Isra'ila sun kutsa farfajiyar masallacin ta kofar Al Magaribe.
Yahudawan sun tada zaune tsaye a yayinda Falasdinawa ke tada kabbarar Sallah, haka kuma 'yan sandan Isra'ila sun kame Falasdinwa hudu.
Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi a jiya a shafukansu na sadar da zumunta suka dinga kira a kai farmaki a Masjidul Aksa.
Masjidul AKsa dai ya kasance alkiblar Musulmi na farko.
Majid Aksa da ya kasance mai guraren ibada, gurin kayan tarihi, Yahudawa na gudanar da aikin tono da sunan cewa wai akwai "Tubalin Sulaiman" a karkashinsa.