Yahudawa 'yan kama guri zauna sun kaiwa wani gidan Falasdinawa hari a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaya.
Majiyoyin yankin sun bayyana cewa, 'yan kama guri zauna sun kai hari gidan wani Bafalasdine mai suna Mutez Al-Kasrawi da ke unguwar Huware a garin Nabulus na Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Ba a jikkata kowa ba sakamakon harin, amma an farfasa gilasan gidan tare da lalata kofarsa.