Yaduwar Rikicin KDP-PKK

Yaduwar Rikicin KDP-PKK

A 'yan makonnin da suka gabata kungiyar ta'addar PKK da sojojin Turkiyya suka gasawa aya a hannu a farmakan kambori-damisa da suka gudanar, sun fara kalubalantar dakarun Gwambatin Kurdawan Arewacin Iraki musanman KDP.

A yayin da Peshmerga da wasu dakaru na musamman da ke da alaka da su, wadanda suka kewaye sansanonin ta’addancin PKK a yankin, suka matsa lamba kan PKK, yarjejeniyar tsakanin Erbil da Baghdad game da kauda PKK daga Sinjar ta haifar da matukar girgizar kungiyar. Bugu da kari, a yayinda kungiyar HPG mai alaka da PKK ke kaiwa dakarun Peshmerga hari kai tsaye a lraki, bangaren kungiyar a Siriya wato YPG ta rinka kaiwa dakarun Peshmerga farmaki a iyakokin kasar. Haka kuma sun kaiwa ofisoshin jam’iyyar ENK a Siriya wacce ke kusa da jamiyyar KDP hari inda suka ma kone wasunsu.

Akan wannan maudu'in mun kasance tare da Mal Can ACUN manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA.

Gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki ta jima tana hakuri da PKK a yankin. Kungiyar, wacce aka yi amfani da ita wajen yaƙi da DAESH, ta yi fice tare da ayyukanta a Arewa maso Gabashin Siriya. Kungiyar ta'addar PKK mai labewa karkashin sunan Kurdawa na kokarin bayyana kanta a matsayar wacce ba ta tabuwa. Duk da irin namijin kokarin da Turkiyya ta yi, gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki ta kasa daukar matakan dakile kungiyar PKK. A ‘yan watannin nan ma Gwamnatin Kurdawan Iraki musanman ma KDP kokarin kare narkad da PKK suka yi. Duk da irin farmakan kambori-damisa da Turkiyya ta kaddamar akan kungiyar ta’addar PKK da aka yi nasarar tarwatsa ta da yawa a wasu gurare ta kasance tana sauya sabon sallon lamurkan da take yi a ko wace rana a iyakokin Iraki. Kungiyar ta fara janyewa daga kudanci a yankin da KDP keda karfin iko , haka kuma karfin gwiwar da rundunar sojan Turkiyya suka nuna a yankin ya sanya kungiyar zargin cewa KDP na taimakawa Turkiyya lamarin da ya sanya ta fara yi musu baranaza.

 

Bugu da kari a Sinjar inda aka yi yarjejeniya tsakanin Erbil da Baghdad an fara ganin kalubale, lamarin da ya sanya aka dauki matakan da suka dace. A yayinda da barazanar suka karu, sun kara kaimin harin da suke kaiwa Peshmerge. Da haka suke tunanin ko KDP za ta janye daga yankin.

Yunkurin PKK na fasa bututun mai a daidai lokacin da gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki ke cikin matsalar tattalin arziki ya kara tsananta lamarin. Shugaban kasa Nejirvan Barzani da firaiminista Mesrur Barzani sun kara daukar kwararar matakn yaki da PKK inda suka kara hadin gwiwa da Turkiyya. Dakarun Peshmerge sun fara kewaye sansanonin ‘yan ta’addan dake Arewacin Iraki. Lamarin dake sanya afkuwar arangama tsakanin dakarun Peshmerge da PKK.

Shugabannin KCK / PKK sun kara samun damar kalubanatar KDP  ta hanyar yin kira ga jama'ar Kurdawa. Daga karshe kuma suka kara kaimin mamabobinsu a Siriya. Da farko sun fara kalubalantar ENSK mai alaka da KDP a Haseke inda suka bude wa ofisoshinsu wuta suka kuma konesu. Daha bisani kuma YPG ta kai wa Peshmerge hari kai tsaye a Fishabur.

A halin yanzu dai ana daf ga barkewa da yaduwar rikici tsakanin bangarorin. Mesrur Barzani ya bayyana cewa ba wai PKK/KCK kawai ba har ma bangarorinsu dake Siriya za a fatattakesu. Akan hakan ya yi kira ga Amurka.  Ya bayyana cewa ya kamata a karya tasirin Qandil a Siriya. Gwamnatin Kurdawan Arewacin Iraki daga karshe dai ta fahimci gaskiyar barazanar PKK. KDP wacce ta rasa damar farmakan kan iyaka da Turkiyya ta kai ta kasance wacce ake kalubalanta kuma wacce ake ganin tana daf ga rasa Sinjar a Iraki.

Wannan sharhin Mal Can ACUN ne manazarcin harkokin waje a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA.


News Source:   ()