Hukumar leken asiri ta kasar Turkiyya (MIT) ta sanar da kame wani kusungumin dan ta’adda dake boye a kasar Yukiren.
Hukumar leken asirin kasar Turkiyya ta gano cewa shahararren dan ta’addan mai suna Isa Ozer ya kasance yana buya a yankin Bahar Asuwad ta gefen Odessa inda yake ci gaba da shirya ta’addanci.
Hukumar ta MIT ta kameshi a cikin wani shiri na musanman inda ta garzaya dashi zuwa Istanbul a cikin wani jirgi na musanman.
An mikashi a hannun hukumar ‘yan sandan dake kula da lamurkan ta’addanci a birnin Istanbul. Ana dai zarginshi da laifuka da dama da suka hada harda shirya ayyukan ta’addanci.
Özer wanda ya shiga kungiyar ta’addar PKK wacce tak eleman kungiyar KCK a shekarar 1996 ya kasance mamaban kungiyar dake goyon bayan PKK a Romaniya mai kuma aikata zamba cikin aminci.