Yabo daga Pakistan ga matsayin Erdogan game ƙyamar Musulunci

Yabo daga Pakistan ga matsayin Erdogan game ƙyamar Musulunci

Pakistan ta bayyana cewar ta yaba irin matsayin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya nuna game da kyamar Musulunci.

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Waje ta Pakistan ta fitar, an bayyana cewar Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Shah Mahmood Qureshi da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu sun tattauna ta way tarho kan ci gaban alakar kasashen biyu da kuma moriyar juna. 

A sanarwar an bayyana cewar Qureshi ya yaba matsayin shugaba Erdogan game da karuwar kyamar Musulunci kuma Cavusoglu ya ce bayanin da Firaministan Pakistan, Imran Khan ya yi game da kyamar Musulunci ya cancanci yabo.

A wani gefe kuma, Qureshi ya jaddada godiya ga kokarin Turkiyya wajen cire kasar Pakistan daga jerin kasashen da Hukumar Hana Safarar Kudade (FATF) ke sa ido a kai.

Qureshi a sanarwar ya kuma taya Turkiyya da al’ummarta murnar bukin Ranar Jamhuriya ta 29 ga Oktoba. 

 


News Source:   ()