Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya (TBMM) Mustafa Sentop, ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin Isra’ila ta fahimci cewa ba za ta iya danne hakki da bukatun Falastinawa ta hanyar amfani da karfi ba, kuma ya kamata ta yi watsi da ta’addancin da take aikatawa a yankin.
Mustafa Sentop ya aike da sakon bidiyo zuwa ga Babban Taron Kungiyar Hadin Kan Yan Majalisu na kasa da kasa (PAB) karo na 142.
Sentop ya bayyana cewa yayin da duniya ke kokarin shawo kan matsalolin da sabon nau'in kwayar cutar Coronavirus (Kovid-19) ya haifar, babban abin kunya ne ga bil'adama har yanzu ana samun labarai na ta'addanci da rikici daga wasu yankuna.
"Rikicin da fararen hula marasa laifi ke fuskanta yayin addu'o'insu a Falasdinu da kuma laifukan cin zarafin bil'adama da aka yi a Gaza sun daskare jininmu."
Mustafa Sentop ya jaddada cewa yayin da ya kamata Isra’ila ta kawo karshen matsayinta da ke yin biris da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da mamayar da take yi ba bisa ka’ida ba a yankunan kasar Falasdinu, ya kara da cewa babu yadda za'a amince da irib cin zarafin da isra'ila ke yi wa al'umman Falasdinawa a lokuttan ibadu da bukukuwan addin kamar Eid al-Fitr.
Sentop, a cikin sakonsa, ya nanata cewa:
"Ya kamata gwamnatin Isra'ila ta fahimci cewa ba za ta iya danne halattattun hakkoki da bukatun abokanmu kuma yan uwanmu Falasdinawa ta hanyar amfani da karfi ba, kuma cikin gaggawa ya zama wajibi tayi watsi da ta'addancinta na kasa. Haka kuma domin kar Isra'ila ta sake maimaita wadannan hare-hare a yankunan Falasdin, kasashen duniya ya kamata su yi watsi da tsarinta da daina bayar da goyon baya ga Isra’ila. Su kuma dauki matakan kawo karshen matsalar yankin bisa daidaito"