Ya zama wajibi ga Amurka ta yi hadaka a Turkiyya domin yaki da ta’addanci

Ya zama wajibi ga Amurka ta yi hadaka a Turkiyya domin yaki da ta’addanci

Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya ya yi kira ga Amurka da ta yi hadaka da Turkiyya akan yaki da ta’addanci a Siriya a maimakon kungiyoyin ta’addanci YPG/PKK.

Minista Hulusi Akar ya bayyana cewa Turkiyya ta magance ‘yan ta’addan Deash dubu 3,700.

Akar ya kara da cewa, a maimakon kungiyar YPG/PKK,  ya zama wajibi ga Amurka ta yi hadaa da yar uwarta Turkiyya a NATO wace ta kasance mambar kungiyar na stawon shekaru 70  ında ya kara da cewa hadaka da Turkıyya akan yaki da ta’addanci lamari ne da Amurka ya dace ta yi kuma Turkiyya ta shiryawa hakan.

A yayinda Akar ke jawabi a ranar tunawa da nasarar Canakkale da mazan jiya ya bayyana cewa YPG da PKK dan juma ne da dan jumai.


News Source:   ()