Ya zama wajibi a yi bincike akan laifukan yakin da Armeniya ta aikata a Nagorno-Karabakh

Ya zama wajibi a yi bincike akan laifukan yakin da Armeniya ta aikata a Nagorno-Karabakh

Kwamitin kare hakkokin bil adama ta majalisar kasar Turkiyya ta yi kira ga Majalsar Dinkin Duniya da ta kafa kwamitin da zai yi bincike akan laifukan yakin da Armeniya ta aikata a Nagorno-Karabakh.

Kwamitin da ta ziyarci yankin Nagorno-Karabakh da wasu sassan Azaibaijan ta lura da cewa Armeniya ta kai hare-haren kalubalantar gidajen farar hula, asubitoci, makabartu, makarantu da guraren kasuwanci.

Ire-iren laifukan yankin da Armeniya ta aikata a yankin Nagorno-Karabakh na bukatar kwamitin Tarayyar Turai ta lura dashi tare da sanya ayi bincike da gabatar da shi a gaba kotun hukuntu laifuka ta kasa da kasa.

Sojojin Armeniya sun kuma dasa bama-baman da ka iya tashe tare da hallaka al’umma duk da an kawo karshen rigimar da ake yi a yankin.

Bugu da kari, kasar ta yi yunkurin kaiwa yankin farar hula a Ganja hari da makamai masu linzami har sau biyu.


News Source:   ()