Ya zama wajibi a hukunta Isra'ila

Ya zama wajibi a hukunta Isra'ila

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ce tsokanar da Isra'ila ke yi wani bangare ne na yakin neman kawar da wasu kabilu, addini da al'adu.

Mevlut Cavusoglu ya halarci Zama na Musamman na Falasdinu wanda Majalisar Kare Hakkin Dan-Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta shirya ta yanar gizo.

Cavusoglu, da yake jawabi akan take hakkin bil adama da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa da kuma mamayar da take yi wa  Masjid al-Aqsa, ya bayyana cewa,

"(Ayyukan Isra'ila) Wadannan tsokanar wani bangare ne na kanfen din kauda wasu kabilu, addini da al'adu." 

"Dole ne mu nemo ingantattun hanyoyi don kawo karshen rashin hukuncin da Isra'ila ke fuskanta." "Babu wata hujja game da hana bil adama zagayawa a Gaza. Dole ne a kawo karshen wannan ta'asar da Isra'ila ke yi a Gaza"


News Source:   ()