An sanar da cewa wani ma'aikacin asibiti a kasar Italiya ya kwashe shekaru 15 bai zuwa wurin aiki kuma ya cigaba da karbar albashinsa.
An sanar da cewa a wani asibitin Ciaccio dake garin Catanzaro wani ma'aikaci ya kwashe shekaru 15 tun daga shekarar 2005 bai zuwa wajen aiki.
A shekaru 15 da yayi bai zuwa wajen aiki ya karbi albashi har na Euro dubu 538 kimanin Naira miliyan 250.
Kamar yadda kanfanin dillancin labaran Italiya ta Ansa ta rawaito, an fara binciken ma'aikacin akan tuhumarsa da laifin aikata cin hanci da rashawa da kuma sabawa kaidar aiki.
Hadi da mai laifin an kuma fara binciken wasu ma'aikatan asibitin har su shida.
'Yan sanda sun kuma zargi mutumin da bai zuwa wajen aikin da yin barazana ga ma'aikatan da suka nemi kam shi da laifin hakan.
An bayyana cewa ma'aikacin ya yi ritaya amma wadanda suka zo bayansa basu lura da hakan ba inda suke zargin ko rashin zuwa wajen aiki ne kawai bai yi.