Wutar dajin Los Angeles ta fantsamu a yankuna 5 bayan ƙone gidaje fiye da dubu

Wutar dajin Los Angeles ta fantsamu a yankuna 5 bayan ƙone gidaje fiye da dubu

Fiye da mutane dubu 100 mahukuntan Amurka suka tilastawa barin yankunansu a birnin na Los Angeles bayan da wutar dajin ta lalata gidaje aƙalla dubu guda ciki har da wasu sassa na tsaunukan Hollywood, a gefe guda kuma wutar ta sake farwa tsaunukan Foothills inda a nan ma ta lalata wasu gine-gine fiye da dubu da ke gab da Altdena da Pasadena na arewacin LA.

Sassa 5 na jihar California wutar dajin ta fantsama ,inda masana ke ganin ibtila’in ka iya haddasa LA asarar dala biliyan 50 a wani yanayi da wutar ke saurin faɗaɗuwa saɓanin yadda aka saba gani musamman a tsaunukan Hollywood.

Wutar dajin ta LA na zuwa a lokacin da wasun California musamman kudancin ke cikin yanayin sanyi matuƙa, ko da ya ke masanan sun ce dama yanayin faruwar gobarar dajin ya sauya zuwa fiye da ruɓanye biyu idan an kwatanta da shekarun 1970.

Cikin watanni 8 da suka gabata, kudancin California ya yi fama da ƙarancin zubar ruwan sama duk da yadda yankin a baya ke sahun masu ganin zubar ruwan sama matuƙa, kazalika, jihar ta ga tsananin zafi tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban bara, dukkaninsu matakan da masana ke alaƙantawa da yadda ɗumamar yanayi ta kai ƙololuwa a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)