A makon da ya gabata shugaban hafsan sojojin kasar Armenia ya nemi firaiministan kasar Nikol Pashinyan da ya yi murabus. Lamarin da Pashinyan ya bayana a matsayin yunkurin juyin mulki da kuma yunkurin cire shugaban hafsan sojojin daga mukaminsa tare da kira ga alumma dasu bayyana akan tituna. Masu goyon bayan gwamnatin kasar da yan adawa sun fara taruwa a Evrim lokaci daya. Kasancewar yadda shugaban kasar bai amince da tube hafsan sojojin kasar daga mukaminsa ba ya sanya Pashinyan ganin cewa shugaban kasar nada hannu a yunkurin juyin mulkin.
A wannan makon mun kasance tare Ferfesa Murat Yesiltas Daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam watau SETA…
Ana ganin cewa akwai dalilai you da suka haifar da maslahohin Armenia. Na farko dai shi ne talauci cin hanci da rashawa. Wannan matsalar duk da dai baida da alaka da Pashinyan ya kasa samar da mafita ga matsalolin gwamnatin kasar. A shekarar 2018 da da Pashinyan ya hau kan karagar mulki ya kusanci kasashen yamma tare da yin akawarin kawo karshen matsalolin talauci da cin hanci da rashawa. Bugu da kari kasancewar masu alaka da Rasha sun kasa samar da mafita ga matsalolin kasar ya sanya ganin fata ga Pashinyan.
Dalili na biyu kuwa shi ne nasarar da Azerbaijan ta samu akan Armenia a yakin Karabakh. Armenia ta kasance ta na mamayar yankin na tsawon shekaru inda aka kasa cimma matsaya ta hanyar diflomasiyya. Kasancewar yadda Pashinyan ya kasance cikin matsin lamba ya sanya shi watsi da matakin "sulhun kasa" inda ya zabi sabuwar "tsarin yaki"
Akan hakan ne aka fara yakin Karabakh da ya tilastawa Armenia ficewa daga yankunan da take mamaya. Pashinyan da yaki bayyana alumman kasar gaskiyar lamari tun tashin fari da kuma kin bayyana a talabijin yayinda yake jawabin ranar 10 ga watan Nuwanba ya baiwa ýan kasar matukar mamaki. Hakika yakin Karabakh na biyu ya kasance mawuyaci ba wai ga sojojin kasar kawai ba, har ma ga Pashinyan da siyasar alumma kasar.
Dalili na uku kuwa shi ne rikicin mallakar iko da banbance banbance raayi a kasar. Akwai wadanda ke da raayin kara mallakar yankin Karabakh. Sun kasance masu hadaka dawasu kasashe ta hanyar Armenia mazauna kasashen waje.
Wannan yunkurin ka iya rage gwagwarmaya makalar iko a kasar tsakanin kasar Rasha da kasashen yamma.
A halin yanzu ana ganin cewa Pashinyan zai iya kare mukaminsa amma hakan baya nufin samawa kasar tsanaki a siyasance. Dalilai ukun da muka zayyana a baya zasu ci gaba da kasancewa tubalin matsalar kasar ga duk wanda zai kasance saman mulki ya Allah Pashinyan ko kuma waninsa.
Wannan sharhin Ferfesa Murat Yesiltas ne Daraktan harkokin tsaro a Gidauniyar Nazarin Siyasa, Tattalin Arziki da Hallayar Dan Adam wato SETA dake nan Ankara babban birnin kasar Turkiyya…