Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar za su raba kunshin kayan gwajin cutar Corona cikin sauri guda miliyan 120 ga kasashe matalauta.
Ghebreyesus ya gudanar da taron manema labarai ta hanyar sadarwar bidiyo a helkwatar Hukumar da ke birnin Geneva na kasar Swizalan.
Ya ce, a karkashin yarjejeniyar da suka kulla da abokan huldarsu, za su bayar da kunshin kayan gwajin cutar Corona cikin sauri guda miliyan 120 ga kasashe matalauta.
Ghebreyesus ya ci gaba da cewa kayan gwaji za su dinga bayar da sakamakon cikinn mintuna 15 zuwa 20.
Ya ce "Ya ce kowanne kunshi ya kai dala dubu 5. Muna sa ran farashinsu zai yi kasa da na PCR."
Ghebreyesus bai bayyana wadanne kasashe za su raba wa kayan ba.