Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar akwai yiwuwar nan da karshen shekara a samu riga-kafin cutar Corona (Covid-19).
Ghebreyesuz ya yi jawabi bayan kammala taron Hukumar Gudanarwa WHO kan yaki da Covid-19 da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Swizalan.
Ya ce "Muna bukatar riga-kafin Corona, kuma muna sa ran akwai yiwuwar nan da karshen shekara a samu riga-kafin cutar."
Ghebyesus bai bayyana yaushe za a fara yin allurar riga-kafin ba a duniya baki daya.
Kamar yadda ya saba a koyaushe, Ghebreyesus ya yi kira ga kasashe da shugabanninsu da su bayar da goyon baya, kuma idan an samu riga-kafin a raba bisa adalci a tsakanin kasashen duniya.
WHO na da manufar raba alluran riga-kafi biliyan 2 nan da karshen shekarar 2021 mai zuwa.