WHO ta yi gargaɗi kan ƙaruwar cutar amai da gudawa a duniya

WHO ta yi gargaɗi kan ƙaruwar cutar amai da gudawa a duniya

Shugaban hukumar Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan yana mai cewa abin tashin hankali ne yadda cutar ke ƙara mamaya dai-dai lokacin da hankalin mahukunta ke kan wasu abubuwan daban.

Ya ce a bara kaɗai adadin waɗanda cutar ta kashe ya ƙaru da kaso 71 cikin 100 idan aka kwatanta da 2022, yayinda adadin waɗanda suka harbu ya ƙaru da kaso 13 cikin ɗari.

Ghebreyusu ya fayyace cewa a 2023 cutar ta harbi mutane 342 cikin su guda 2,400 sun hallaka a sassan duniya.

Hukumar ta cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ƙaruwar cutar ya haddasa ƙarancin rigakafinta, kuma an ga yadda  ƙasashe suka buƙaci rigakafin cutar da ba’a taɓa ganin yawan haka ba cikin shekaru 10 da suka gabata.

WHO ta ƙara da cewa tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023 ƙasashen duniya sun karɓe kafatanin rigakafin cutar guda miliyan 36 da aka samar abinda aka jima ba’a ga irinsa ba.

Wannan ce ta sa hukumar ta buƙaci hukumomin lafiya da kuma ƙasashen duniya da su sanya idanu sossai kan cutar da kuma lalubo hanyoyin tunkararta cikin gaggawa ta hanyar samar da tsaftataccen ruwan sha da sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)