Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi da a kula sosai bayan wa'adin kwanaki 10 na raguwar kamuwa da cutar Corona a nahiyar Turai ya kare.
Daraktan WHO na Turai Hans Kluge ya fitar da sanarwa game da halin yaduwar Corona ya ke a najiyar.
Kluge ya ce, bayan karewar wa'adin kwanaki 10 na raguwar kamuwa da Corona a Turai tare da saukaka al'amura da bayar da izinin yin tafiya, a makon da ya gabata an samu karin masu dauke da cutar da kaso 10 cikin dari.
Jami'in na WHO ya kuma ce, idan ba a ci gaba da daukar matakan yaki da cutar ba, akwai yiwuwar yaduwar ta da yawa ya sake karuwa.