WHO ta yabawa Turkiyya

WHO ta yabawa Turkiyya

Daraktan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) na Turai Dakta Hans Kluge ya yabi Turkiyya.

Sanarwar da Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya ta fitar ta ce, Minista Fahrettin Koca ya tattauna da Kluge ta hanyar sadarwar bidiyo.

A ganawar an tabo batutuwan karuwar kamuwa da Corona a Turai, sauyawar cutar da kuma halin da ake ciki a Turkiyya.

Kluge ya shaida cewar, yana taya Turkiyya murna bisa ci gaba da aiyuka da shawarwarin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya da ta ke yi.

Ya ce "Dukkan kasashe na yabawa irin aiyukan da ake yi karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. Ina taya ku murna saboda irin tsarin samar da bayanai mai kyau da ku ke da shi. Haka zalika ina taya ku murna sakamakon aiyukan samar da riga-kafi da ake yi a Turkiyya, aiyukan kwayoyin halittar cutar da yadda su ke da kuma samar da kayan gwaji cikin sauri da kuka yi."

 


News Source:   ()