Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta sauya sunayen sabbin nau'ikan cutar Corona (Covid-19) da aka gano a kasashen duniya daban-daban.
Sakamakon bukatar da kasashen suka nema, an baiwa sabbin nau'ikan cutar wasu sunaye na daban maimakon kiran su da sunan kasashen da suka fito daga ciki.
Karkashin hakan za a dinga kiran sabon nau'in Corona na ingila da sunan "Alfa", na Afirka ta Kudu "Beta", na Barazil "Gamma", na Indiya guda 2 kuma "Delta" da "Kappa" sai na Amurka guda 2 da aka bawa sunayen "Epilson" da "Iota".
Manufar wannan mataki ita ce a kawar da nuna wariya ga kasashen da sabbin nau'ikan Corona ya fito.