WHO ta kafa gidauniyar tara kudaden da za su cike giɓin da Amurka ta haifar mata

WHO ta kafa gidauniyar tara kudaden da za su cike giɓin da Amurka ta haifar mata

A watan Janairun da ya gabata ne, Donald Trump, ya rattaɓa hannu kan wasu gomman dokokin zartawa na ikon shugaban ƙasa, ciki har da janye Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris.

Tania Cernuschi, mai shekaru 46, wadda itace jami’ar Hukumar da ta bude wannan asusu, ta ce ficewar Amurka daga WHO da Donald Trump ya yi, shakka babu ya haifar da giɓi mai girma ga hukumar.

A ranar Laraba, itama kasar Argentina ta fitar da sanarwar ficewarta daga WHO din, abin da ake ganin shima zai kawo cikas ga ayyukan hukumar.

Karo na biyu kenan da Trump ke fitar da Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma yarjejeniyar yanayi ta birinin Paris da aka cimma a shekarar 2015, domin rage gurɓatacciyar iska, kafin Joe Biden ya sake mayar da ƙasar cikinta.

Da yake kare matakin janye ƙasar daga WHO, Mista Trump ya ce Amurka ke bayar da kaso 20 cikin ɗari na kudin gudanarwarta, amma ta gaza taɓuka abin azo a gani, masamman bayan ɓarkewar annobar Corona.

Bayaga dokoki da suka shafi shigar baƙi ƙasar da kuma tsugunnar da 'yan gudun hijira, sabon shugaban na Amurka ya dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bai wa  ƙasashen waje har tsawon kwanaki 90, domin sake nazari a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)