Shugaban Hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X, ya ce asibitin wanda ya kasance tilo a El Fasher, na dauke da bangarorin kula da lafiyar mata, sashen tiyata, bawa kananan yara kulawa da kuma cibiyar samar da abinci mai gina jiki ga masu fama da cutar yunwa sai kuma sashen samar da magunguna.
Sanarwar daraktan na WHO ta ci gaba da cewa, za su ci gaba da yin kira da a dakatar da kai hare-hare kan harkokin kiwon lafiya a Sudan, da kuma ba da damar maye gurbin kayayyakin da suka lalace cikin gaggawa.
Yakin da aka gwabza tsakanin sojojin Sudan da ‘yan tawayen RSF, wanda ya barke a watan Afrilun 2023, ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane, inda miliyoyi suka tsere daga gidajensu, abin da ya jefa rabin al'ummar kasar cikin tsananin yunwa.
Rikicin ya haifar da tashin hankali na kabilanci da aka fi dora alhakinsa kan kungiyar RSF.
Gwamnan Darfur Mini Minnawi ya wallafa a shafinsa na X cewa wani jirgin sama maras matuki na RSF ya kai hari a sashen bayar da agajin gaggawa na asibitin da ke babban birnin arewacin Darfur, inda ya kashe marasa lafiya da suka hada da mata da yara.
An yi kazamin fada a El Fasher tsakanin RSF da dakarun hadin gwiwa na Sudan, da suka hada da sojoji, kungiyoyin gwagwarmaya masu dauke da makamai, 'yan sanda, da kuma jami'an sa kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI