WHO ta bayar da izinin a yi amfani da allurar riga-kafi da Pfizer-BioNTech suka samar

WHO ta bayar da izinin a yi amfani da allurar riga-kafi da Pfizer-BioNTech suka samar

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayar da izinin a yi amfani da allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) da kamfanunnukan Pfizer-BioNTech suka samar.

WHO ta fitar da sanarwa mai muhimmanci, shekara guda bayan da ta sanar da bullar cutar sarke numfashi a garin Wuhan na kasar China.

Rubutacciyar sanarwar da Kungiyar ta fitar awanni kadan kafin karewar shekarar 2020, ta ce, ta bayar da izinin a yi aiki da allurar riga-kafin da kamfanin Jamus na Biotechnology mallakin Farfesa Ugur Sahin da kamfanin Pfizer na Amurka suka samar.

Mataimakiyar Darakta Janar na WHO Dr. Mariangela Simao ta sanar da cewa

"Wannan nataki ne mai kyau yadda dukkan duniya za su samu allurar riga-kafin."

 


News Source:   ()