WHO ta amince da a yi amfani da allurar riga-kafin Corona ta Sinovac

WHO ta amince da a yi amfani da allurar riga-kafin Corona ta Sinovac

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta amince da ayi amfani da allurar riga-kafin cutar Corona (Covid-19) ta Sinovac da aka samar a China.

Allurar da aka amince a yi wa 'yan shekaru 18 zuwa sama, ana karbar ta sau 2 da tazarar makonni 4.

Ba a bayyana shekaru mafi yawa na wadanda ba za a iya yiwa allurar ba.

WHO ta sanar da cewa, riga-kafin Sinovac na bayar da kariya ga munanan cututtuka da kwanciya a asibiti, kuma allurar na bayar da riga-kafi daga nuna alamun kamuwa da Corona.

Hukumar ta Lafiya ta Duniya ta kuma bude kofar yadda za a fara amfani da allurar riga-kafin Sinovac a kasashe matalauta a karkashin shirin COVAX.

Ya zuwa yanzu WHO ta amince da a yi amfani da alluran riga-kafi har guda 8.


News Source:   ()