WHO: Muna bincike kan wadanda suke dauke da Corona amma ba sa nuna alamunta

WHO: Muna bincike kan wadanda suke dauke da Corona amma ba sa nuna alamunta

Sakatare Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar suna ci gaba da gudanar da bincike kan ko ana daukar cutar Corona daga jikin mutanen da suke da ita amma kuma ba sa nuna alamunta.

Ghebreyesus ya gudanar da taron manema labarai ta hanyar bidiyo a birnin Geneva na kasar Swizalan inda ya cutar Corona wata cuta ce sabuwa da ba a san ta ba a baya.

Ya ce "Mun koyi abubuwa da dama amma har yanzu akwai abubuwan da ba mu sani ba."

Ghebreyesus ya kara da cewar a kowanne mako suna ganawa da kasashe mambobin WHO da kuma kafafen yada labarai inda suke bayyanawa duniya halin da ake ciki game da cutar Corona (Covid-19).

Da ya ke tabo batun shin ko ana iya kamuwa da cutar corona daga jikin wadanda suke dauke da ita amma ba sa nuna alamun suna da ita, Ghebreyesus ya ce "Tun watan Fabrairu muka fadi cewar wadanda ba sa nuna alamun suna dauke da Corona na iya harbawa wasu, amma muna ta gudanar da bincike don ganon karfin iya harbawa wasun."


News Source:   www.trt.net.tr