Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar suna adawa da duk wani nau'i na nuna wariya da bambanci a duniya.
Ghebreyesus ya gudanar da taron manema labarai ta hanyar sadarwar bidiyo a helkwatar Hukumar da ke birnin Geneva na kasar Swizalan.
Ghebreyesus ya tabo batun kisan bakar fata George Floyd da 'yan sanda Amurka suka yi bayan sun kama shi a ranar 25 ga watan Mayu wanda ya janyo zanga-zanga a fadin duniya inda ya ce "WHO tana goyon bayan adalci da adawa da nuna wariya a duniya. Muna adawa da duk wani nau'i na nuna wariya."
Ghebreyesus ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar da ake yi fadin duniya cikin tsaro da lumana.
Ya ce "Ya kamata a dinga bayar da tazara akalla ta mita 1 a tsakanin masu zanga-zangar. Kuma Idan mutum yana tari ko atishawa a wajen to ya tabbatar ya saka takunkumin rufe baki."