WHO: Korona za ta fi sanadiyar rayuka a shekarar 2021 fiye da bara

WHO: Korona za ta fi sanadiyar rayuka a shekarar 2021 fiye da bara

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa a shekarar 2021 za'a fi samun "mace-mace" sakamakon kamuwa da kwayar cutar (Kovid-19), wacce ta bulla a cikin kasar China a karshen shekarar 2019 kuma ta rikide zuwa annoba ta hanyar yaduwa a duk duniya a cikin 2020.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta-Janar na WHO ne ya sanar da hakan inda ya kara da cewa,

"Mun yi imanin cewa shekara ta biyu ta wannan annoba za ta fi harfar da mace-mace fiye da yadda ta haifar a shekarar farko." 

Ghebreyesus ya bayyana cewa hawa na biyun annobar a Indiya "yana da matukar damuwa", Ghebreyesus ya kara da cewa a bulluwar cutar a karo na biyu a kasar Indiya an samu karin yawan wadanda suka kamu da cutar, kwantawa asibiti da mace-mace fiye da lokacin ta farko a mafi yawan jahohin dake fadin kasar"

Ghebreyesus ya bayyana cewa a matsayin WHO, sun aika da bututun iskar oxygen zuwa Indiya, tanti, abin rufe fuska da kayan aikin asibiti don amfani a asibitocin wuccin gadi dake fili.


News Source:   ()