Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, a tsawon kwanaki 7 a jere kamuwa da cutar Corona a duniya baki daya na raguwa wanda hakan ne raguwa mafi yawa tun farkon bullar cutar.
A taron manema labarai da Ghebreyesus ya gudanar a Ofishin Hukumar da ke birnin Geneva ya bayyana cewa, kafin a gudanar da taron G7 a Jamus a 2022 suna da manufar yiwa kaso 70 na al'umar duniya allurar riga-kafin Corona.
Ya ce, "Domin samun wannan nasara muna bukatar allurai biliyan 11."
Darakta Ghebreyesus ya yi nazari tare da lura kan halin da ake ciki game da yaduwar Corona a duniya baki daya inda ya ce, a tsawon kwanaki 7 a jere ana samun raguwar kamuwa da cutar kuma ya zuwa yanzu wannan ne lokaci mafi tsawo a jere da hakan ta faru.
Ghebreyesus ya ce, "Duk da wannan ne lokaci na mako da aka samu mafi karancin kamuwa da cutar, amma rasa rayuka kuma ba ya raguwa. Rasa rayuka na makon da ya gabata kusan daya ne da na makon da ya gabace shi. A kowanne kwanaki 10 sama da mutane dubu 10 suna mutuwa. A lokacin da muke wannan taro sama da mutane 420 ne za su mutu."
Ya kara da cewa, a kasashe da dama ana samun raguwar kamuwa da cutar amma kuma rasa rayuka na da ban tsoro a kasashen.
Ya ce, "Musamman a Afirka ana fargaba sosai na karuwar rasa rayuka. Saboda a wannan waje babu alluran riga-kafi, ba a yin gwaji kuma babu na'urorin taya numfashi yadda ya kamata."