Wakilin Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) kan yaki da cutar Corona Dr. David Nabarro ya yi gargadi da cewar, matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, to za a iya shiga zagaye na 3 na yaduwar cutar Corona (Covid-19) a duniya.
Labaran da aka fitar a shafin yanar gizo na Swissinfo na cewa, David Nabarro ya tattauna da kafar yada labarai ta Jamus ta CH Media a Swizalan inda ya soki yadda Swizalan da Turai su ke yaki da annobar Corona.
Nabarro ya bayyana cewar, sassauta matakan yaki da cutar Corona da kasashen Turai suka dauka ya sanya sun zama a baya sosai, idan aka kwatanta da kasashen Asiya, kuma Swizalan na daya daga cikin kasashen da suka fara sassauta matakan wanda hakan ya sanya ta fadawa cikin wadanda cutar ta dawo da yaduwa sosai a karo na 2 a cikinsu ba tare da sun yi kyakkyawan shiri ba.
Nabarro ya ce, da fari Turai ba ta mayar da hankali yadda ya kamata ba wajen yaki da Corona, kuma ga shi an shiga zagaye na 2 na yaduwar cutar.
Ya ce "Watanni bayan magance cutar da ta fara yaduwa sosai a duniya, da a ce an dauki matakan da suka kamata a lokacin zafi, da ba a shiga zagaye na 2 na yaduwar cutar a yanzu ba. Idan ba a dauki matakan da suka kamata a yanzu ba, to za a shiga zagaye na 3 na yaduwar cutar a nan gaba."