WHO: Daga Jemagu Chinawa suka kamu da Coronavirus

WHO: Daga Jemagu Chinawa suka kamu da Coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya watau WHO ta tabbatar da cewa Chinawa sun fara kamuwa da kwayar cutar Covid-19 daga jemagu kuma annobar ta fara bulluwa ne a kasuwar siyar da kifi da sauran abincin da ake samu daga teku.

Kwararre akan cututtukan da mutane ke dauka daga dabbobi da abinci ta Hukumar WHO Peter Ben Embarek a hirar da ya yi da manema labarai ta bidiyo konferans ya bayyana cewa annobar Coronavirus an dauke ta ne a kasuwar kayayyakin abincin teku dake garin Wuhan a jihar Hubey.

Ya kuma kara da cewa "Lamarin bayyana yake kasuwar ta taka rawa wajen yaduwar wacannan cutar amma bamu san iran rawar da ta taka ba"

Embarek ya nuna cewa farkon cutar na iya kasancewa daga cikin kasuwar ce a Wuhan ko kuma gano ta kwatsam a ciki da wajen kasuwar.

Embarek ya  tabbatar da cewa an kamu da kwayar cutar Covid-19 daga jemagu amma akwai bukatar a kara yin kwararan bincike akan lamarin.

A cewarsa "Ba mamaki an kawo dabbobi ne dauke da cutar a kasuwar ko kuma masu zuwa cin kasuwar da suka kamau da cutar ne suka shigo da ita a kasuwar"

Da yake nuna cewa kasuwannin dabbobi na da matukar muhimmanci wajen samar da abinci da abubuwan more rayuwa ga miliyoyin mutane a duk duniya, Embarek ya yi kira ga hukumomi da su inganta maimakon rufe irin wadannan wuraren.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Ministan Harkokin Waje Mike Pompeo sun yi ikirarin cewa an Covid-19 ya barkene daga dakin gwaje-gwaje a  Wuhan.

A nata bangaren, gwamnatin kasar Sin ta musanta ikirarin cewa an samar da kwayar cutar ne a dakin gwaje-gwaje, kuma ta bayar da hujjar cewa, ana yin siyasa da lamarin.


News Source:   www.trt.net.tr