WHO: Da wuya a samu sahihin maganin Corona

WHO: Da wuya a samu sahihin maganin Corona

Babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar da wuya a iya samun sahihin maganin da zai iya magance kwayar cutar Covid-19 da kawo yanzu ta kama fiye da mutum miliyan 18 a doron kasa.

Daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi bayani a taron manema labarai inda ya bayyana cewa "Da wahala a iya samar da wani sahihin maganin da zai iya kauda Covid-19 baki daya sabili da haka ya na wahala jkwaran gaske lamurka su koma daidai"

Ghebreyesus, ya yi nuni da muhinmancin sanya takunkuman rufe fuska, bayar da tazara daga juna, wanke hannu, inda kuma ya kara da cewa a halin a aikin samar da allurar-riga-kafi an kai mataki na gwaji na uku. A cewarsa muna fatan a cimmma babban nasara akan haka, ya kara da cewa kawo yanzu babu wani riga kafin cutar"

Ghebreyesus, kuma ya yi kira ga iyaye mata su rinka shayar da jinjiransu domin shayarwa na da fa'ida sosai yana kuma rage hastarin kamuwa da cutar.


News Source:   ()