Tawagar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) da ke binciken asalin sabon nau'in kwayar cutar corona a kasar China sun bayyana cewa, kwayar cutar ba ta fito daga dakin gwaje-gwaje ba, akwai babbar yiwuwa tushen cutar jemage ne.
WHO da wakilan kasar China sun sanar da sakamakon binciken a taron manema labarai da suka gudanar a Wuhan.
Wakilan sun bayyana cewar sun kawar da yiwuwar cewa an kirkira kwayar cutar a dakin gwaje-gwaje. An jaddada cewa akwai babbar yiwuwa asalin kwayar cutar jemage ne.
A cewar wakilan, akwai yiwuwa sosai cewa kwayar cutar na iya yaduwa ta daskararren abinci.
Wakilan WHO sun kuma lura cewa ba tabbas cewa kwayar cutar ta fito daga Wuhan, inda ta ja hankali ga shaidar da ke nuna cewa kwayar cutar ta yadu a wajen kasuwar Huanan da ke cikin birnin.
Wakilan na China sun bayyana cewar ba a san daga wacce dabba kwayar ta yadu ba. Sun kuma bayar da hujjar cewa, babu isassun shaida da ke nuna cewa kwayar ta yadu daga garin Wuhan.