WHO: Covid-19 ka iya kasancewa tamkar HIV

Daraktan kullawar Gaggawa ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Mike Ryan ya yi gargadin cewa kwayar cutar Covid-19 ka iya kasancewa dindindin tamkar kwayar cutar HIV.

Ryan, ya amsa tambayoyi a taron bidiyo konferans da suka gudanar a helkwatan hukumar ta WHO dake Geneva tare da shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus.

Ya bayyana cewa kasashe da yawa sun fara sassauta dokar hana fita waje da sauran dokokin da aka kaddamar domin yakar corona, inda ya kara da cewa wannan mataki ne da zai haifar da wahalar magance ko ganin bayan cutar cikin sauki.

Ryan, ya jadadda cewa "Dukaninmu, muna masu matukar damuwa akan irin mummunan da'ira da za ta shafi kiwon lafiyar al'umma da ma tattalin arzikin kasashe matukar aka sassauta dokar yakar Covid-19 gabanin a cimma wata babban nasara"

A yayinda aka tambaye shi game da binciken da ake yi akan allurar riga-kafi, Ryan ya kada baki ya ce,

"Ya kamata mu bayyana cewa ga dukkan alamu wacannan cutar ba za ta kare ba, ba zata ta fi ba, ba za ta kawo karshe ba" Ya kara da cewa,

"Tamkar dai kwayar cutar HIV ganin an samu hanyoyin kariya da wasu magani al'umma basa tsoron cutar kanjamau kamar yadda suke tsoronta a da"

 


News Source:   www.trt.net.tr