WHO: Corona na ci gaba da yin ajalin mutane a duniya

WHO: Corona na ci gaba da yin ajalin mutane a duniya

Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanov Ghebreyesus ya bayyana cewar annobar Corona ba ta raguwa, sabanin haka sai kara bunkasa ta ke. Adadin masu kamuwa da ita da wadanda ta ke kashewa na karuwa a kowacce rana.

Gyebreyesus ya yi bayani ta hanyar sadarwar bidiyo a wajen taron Majalisar Dinkin DUniya kan ranar Ma'aikatan Gwamnati ta kasa da kasa.

A jawabin da Ghebreyesus ya yi ya bayyana cewar "Annobar Corona ba ta raguwa. Tana ci gaba da karuwa a kullum inda wadanda ke mutuwa ke kara yawa."


News Source:   www.trt.net.tr