Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewar "Annobar Corona na ci gaba da karuwa amma ba a kai matakin rasa yadda za a yi da ita ba."
Ghebreyesus ya yi jawabi a taron manema labarai ta hyanyar bidiyo da aka gudanar a helkwatar Hukumar da ke birnin Geneva na kasar Swidin inda ya sake jaddada cewar cutar na yaduwa cikin sauri kuma na janyo asarar rayuka.
Ghebreyesus ya ce watanni 3 bayan cutar ta bulla, ta kama jimillar mutanne dubu dari hudu a fadin duniya.
Ya kara da cewa "A karshen makon da ya gabata kadai an samu mutane sama da dubu dari hudu da suka kamu a fadin duniya. A yanzu cutar ta kama mutane miliyan 11,4 tare da yin ajalin sama da mutane dubu dari biyar da talatin da biyar. Cutar Covid-19 na yaduwa cikin sauri, a bayyana yake karara cewar ba mu kai matakin da za a kasa shawo kanta ba. Duk da za a ga kamar a wasu kasashe ana samun raguwar yaduwarta, amma a wasu kasashen tana ci gaba da daduwa sosai."
Ghebreyesus ya yi gargadi da cewar ba za a dauki cutar da wasa ba, kuma babu kasar da ta ke cikin aminci.