WHO: Babu shaidar sabon nau'in Corona da aka gano a Ingila na kisa da gaggawa

Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanov Ghebreyesus ya bayyana cewar, ba a samu wata shaida da ke tabbatar da sabon nau'in cutar Corona da aka gano a Ingila wanda ke yaduwa cikin sauri, na da hatsari sosai ko kuma kisan mutane da gaggawa ba.

A taron manema labarai da Ghebreyesus ya gudanar ta hanyar sadarwar bidiyo a helkwatar WHO da ke birnin Geneva na kasar Swidin, ya bayyana cewa,

"A 'yan kwanakin nan akwai labarai da suka fito daga Ingila da Afirka ta Kudu dangane da cutar Corona. A wasu lokutan annoba na rikidewa ta sauya yanayi. Wannan abu ne da aka sani kuma ake tsammanin afkuwar sa."

Ghebreyesus ya shaida cewa, tare da wannan nau'İn cutar, c,ikin sauki mutane su ke kamuwa da ita a Ingila inda ya ce "Amma har yanzu ba a samu wata shaida da ke nuna sabon nau'in cutar na da hatsari sosai ko kuma yana janyo mutuwa cikin gaggawa ba."

Bayan da aka sanar da cewar a Ingila cutar Corona ta rikide tare da yaduwa cikin sauri, Firaministan kasar Boris Johnson tare da wasu masanan kimiyya sun bayyana cutar na yaduwa cikin sauri da kaso 70 sama da yadda aka saba gani, Ministan Lafiya na Ingila Matt Hancock kuma ya ce an kasa shawo kan cutar.

Bayan Ingila, an ga bullar wannan nau'i na Corona a Denmark, Ingila da Afirka ta Kudu.

 


News Source:   ()