Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, za a dauki lokaci mai tsawo kafin a iya rabuwa da cutar Corona, amma a cikin 'yan watanni za a iya shawo kanta.
Daraktan na WHO ya shida cewa, duk da allurai miliyan 700 da aka yi a fadin duniya, amma cutar na ci gaba da yaduwa a makonni 7 da suka gabata.
Ghebreyesus ya ci gaba da cewa, "Muna son mu ga an bude tattalin arziki, ana yin tafiye-tafiye da kasuwanci. Amma a yanzu haka asibitocin wasu kasashen sun cika da mutane, kuma ana samun rasa rayuka."
Ghebreyesus ya kuma sanar da cewa, za a dauki lokaci mai tsawo kafin a rabu da cutar Corona a duniya baki daya.
Ya ce, "Akwai dalilai da dama da suke bamu karfin gwiwa da fata nagari. Raguwar kamuwa da cutar da rasa rayuka a watanni 2 na farkon shekara na bayyana za a iya dakatar da sabon nau'in cutar."
Shafin yanar gizo na Worldmeter ya bayyana a duniya baki daya Corona ta yi ajalin mutane miliyan 2 da dubu 951 inda ta kuma kama sama da mutane miliyan 136.