WHO: Annobar Corona za ta kare a farkon 2022

WHO: Annobar Corona za ta kare a farkon 2022

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, annobar Corona (Covid-19) za ta kawo karshe a farkon shekarar 2022, kuma an bar munanan ranaku a baya.

Daraktan WHO na nahiyar Turai Dr. Hans Kluge ya tattauna da tashar DR ta kasar Denmark inda ya bayyana cewar, shekarar 2021 za ta zama shekarar Corona, amma sai an kula sosai sama da shekarar 2020.

Kluge ya kuma ce, an bar munanan kwanaki a baya, an samu bayanai sosai game da cutar sama lokacin da ta fara bulla.

Ya ce "Ina tunanin cutar za ta kawo karshe a farkon 2022."

Kluge ya ci gaba da cewa, Cutar za ta ci gaba da wanzuwa, amma ba na tunanin za a bukaci daukar matakan hana zirga-zirga. Wannan sako ne mai faranta zuciya."

Da ya ke tabo sauya batun kamanni da alamu da cutar Covid-19 ke yi, Kluge ya ce wannan abu ne da aka saba gani tare da cututtuka masu yaduwa, amma suna da fargabar yadda irin wannan nau'i ke yaduwa cikin sauri.

Ya kuma ce, za su ci gaba da bibiyar ganin ko alluran riga-kafin da ake samarwa na da tasiri kan sabon nau'in cutar Corona. Idan akwai bukata, za a dinga samar da alluran yadda za su iya bayar da garkuwa ga sabon nau'in Covid-19.


News Source:   ()